Jami’an tsaro a Jihar Kaduna sun samu nasarar kama mutane 398, tare da kwato tarin makamai daga hannun batagari a Jihar.

Gamayyar jami’an tsaron haɗin gwiwa na musamman da gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamna Malam Uba Sani ta kafa a kokarinta na kawo karshen ayyukan ƴan daba a Jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Jihar Mansur Hassan ya fitar, inda ya ce Jami’an sun kama mutanen ne a sintirin da suka gudanar a gurare daban-daban na Jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa bayan samun bayanan sirrin akan batagarin ne jami’an suka gaggauta daukar mataki akansu.

Kakakin ya ce sumamen da jami’an ke kai’wa kan batagari, hakan ya sanya da yawa daga cikinsu sun bar Jihar domin kaucewa kamun jami’an tsaro.

Masur ya kara da cewa a cikin kwanaki tara da jami’an suka gudanar da ayyukansu, sun kama wani mutum mai suna Mathew Adamu wanda ya kware wajen aikata ta’addan a Jihar.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa gamayyar jami’an sun hada da ’yan sandan, sojoji, DSS, NSCDC, NDLEA,FRSC jami’an hukumar shige da fice ta Kasa, jami’an hukumar gyaran hali, jami’an Hukumar Kwastam, da kuma jami’an tsaron sa-kai.

Kakakin ya ce a cikin wadanda aka kama ciki harda wani mutum mai suna Adamu Umar da aka kama da karamar bindiga, da mai sanar sayar da kayan maye da za a tasa keyarsa zuwa ga hukumar NDLEA.

Bayan kammala bincilke za a gurfanar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: