Ƴan Majalisar Wakilai a Jihohin Neja da Kwara, sun bayyana cewa mutane 600 da suka bace a yayin ambaliyar ruwa a karamar hukumar Mokwa ta Jihar Neja har kawo yanzu ba a gansu ba.

Ƴan majalisar Joshua Audu Gana daga Jihar ta Neja da Dan majalisar daga Jihar Kwara Saba Ahmed Umaru ne suka bayyana hakan ne a gaban zauren majalisar a jiya Laraba.

A yayin zaman ƴan majalisar suka gabatar da kudurin gaggawa, su na masu cewa ambaliyar ba iya Jihar ta Neja kadai ta tsaya ba har zuwa karamar hukumar Edu ta jihar Kwara.

Sun ce bayan trabbatar da mutuwar mutane 500 a sanadin ambaliyar, inda ragowar fiye da 600 suka bace suma za a bayyana su a matsayin wadanda suka mutu duba da babu lamarinsu.

Hadakar ƴan majalisar biyu sun kara da cewa ambaliyar ta lalata gidaje sama da 4,000, mutane 200 suka jikkata, yayin da gonaki, gine-gine, duk suka lalace.

Bayan gabatar da wannan kuduri Majalisar ta yi muhawara da kuma amincewa da kudurin, tare da bayar da umarnin inganta hanyoyin dakile matsalar ambaliya a yankin harma da sauran yankunan da ke cikin barazanar ambaliyar cikin gaggawa.

Sananna majalisar ta umarci Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA da ta samar da kayayyakin agaji da na tsafta ga al’ummomin da lamarin ya shafa domin kaucewa sake barkewar cututtuka.

Majalisar ta kuma yabawa Shugaban Kasa Bola Tinubu bisa bayar da tallafin Naira biliyan biyu ga wadanda lamarin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: