Wasu ’yan ta’addan Lakurawa a Jihar Sokoto sun kai wani hari ƙauyen Kwalajiya da ke cikin Ƙaramar Hukumar Tangaza tare da hallaka mutane 15.

Ƴan ta’addan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 2:00 na ranar Talata, inda ake zargin harin na ramuwar gayya ne suka kai bayan hallaka ƴan Lakurawan uku a yankin ciki harda jagoransu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun mamaye yankin ne a lokacin da mutanen garin ke cikin masallaci suna sallar Azahar.

Mazauna garin sun kara da cewa a yayin harin ƴan ta’addan sun kuma kone kayyakin abinci, gidaje, shaguna da kuma gonaki.

Sannan ƴan ta’addan sun kuma kone na’urorin sadarwar garin , wanda hakan ya haifar da nakasu wajen kira.

Kazalika sun mafiya yawa daga cikin mazauna kauyen sun tsere daga muhallansu domin tsira da rayuwarsu.

Mazau Kauyukan sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu daukin jami’an tsaro, tare da gyara layin sadarwar da suka lalata na yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: