Helkwatar tsaro a Najeriya ta ce babban kwamandan Boko Haram mai suna Ibn Ali ya mika wuya tare da miƙa makamansa.

 

Kwamandan ya mika wuyan ne a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.

 

Daraktan yaɗa labarai na helkwatar Manjo Janar Markus Kangye ne ya tabbatar da haka yau Asabar a Abuja

 

Ya ce jami’an tsaron ƙarƙashin dakarun Operation Haɗin Kai ne su ka kai wasu hare-hare a tsakanin ranakun 4 da 10 ga watan Yuli da mu ke ciki a yankin Platari da ke dajin Sambisa da Timbuktu wajen da yan ta’adda ke da yawa a yankin.

 

Ya ƙara da cewa yan bindiga da yawa da su ka haɗa da maza da mata manya da yara ne su ka miƙa wuya bayan shan matsin lamba daga soji

 

An kai wa ƴan ta’addan harin ne a yankin Gwoza, Mafa Ngala, Abadam, Biu, Konduga da Dikwa da ke jihar Borno sai kuma Madagali da ke jihar Adamawa.

 

Haka kuma an hallaka da yawa daga ciki yayin da su ka kama biyar

 

Sannan akwai makamai da su ka kwato daga yan bindigan.

 

Haka kuma akwai ababen fashewa da su ka gano da kuɗi da ya kai naira 822,500.

 

A cewarsa dakarun soji da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro ne su ka kai hare-haren da su ka kai ga samu nansara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: