Majalisar dokokin Najeriya ta dage zamanta har zuwa ranar 22 ga watan Yuli d amu ke ciki domin alhini ga rasuwar marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Magatakardar majalisar Kamorub Ogunlana ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya sanyawa hannu yau Litinin
A cewarsa majalisar ta dakatar da duk wani zama har tsawon mako guda domin yin alhinin rashin tsohon shugaban ƙasar.

Majalisar dartawa da majalisar wakilai ne su ka bayar da sanarwar dage zaman tsawon kwanakin.

Sannan sanarwar ta umarci dukkan mambobin majalisar da su shirya domin halartar jana’izar tsohon shugaban ƙasar.
Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu a birnin Landan jiya Lahadi bayan ya sha fama da jinya.
Sanarwar ta ce za a ci gaba da tunawa da shugaba Muhammadu Buhari bisa sadaukarwarsa ga kasa d akuma nuna dattako.