Kungiyar malaman jinya da ungozoma ta Najeriya ta dakatar da yajin aikin gargadi da ta tsunduma a Ƙasar a hukumance.

Shugaban kungiyar na Ƙasa Haruna Mamman, da Sakatarenta T.A. Shettima suka sanar da dakatar da yajin aikin a wani taron manema labarai a Abuja yau Asabar.

Mamman ya ce an cimma wannan matsayar ne bayan wani taron gaggawa na majalisar zartarwar kungiyar ta kasa, inda ta yi nazari kan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tare da rattabawa hannu.

A cewarsa gwamnatin tarayya ta amince da aiwatar da dukkan wasu muhimman bukatunta tara da kungiyar ta gabatar mata.

A jiya Juma’a ne dai kungiyar ta gudanar da wani zama da wakilan gwamnatin tarayya kan yajin aikin, inda a yau ta sake yin wani zama kan batun daga bisa ta dauki matakin dakatar da yajin aikin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: