Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya koka kan karancin shayar da jarirai nono a jihar Benue.

Shugabar ofishin UNICEF a Jihar Enugu Misis Juliet Chiluwe, itace ta bayyana hakan a lokacin bikin kaddamar da makon shayar da yara nonon uwa ta duniya na shekarar 2025 a Benue.

Kungiyar ta ce shayarwa itace matakin farko ga yara bayan zuwansu duniya.

Acewarta duk da cewa sama da kashi 90 cikin 100 na iyaye mata a Najeriya na shayar da jariransu, kashi 47 ne kawai a jihar Benue suka fara shayar da jariran a cikin sa’a ta farko na haihuwa.

Yayin da ta ce kashi 56.7 ne kawai ke shayar da nonon uwa na tsawon watanni shida, wanda hakan ya nuna Kasa da abin da ake bukata na kasa da kasa yayin da kashi 37.6 ne kawai ke ci gaba da shayarwa har zuwa shekaru biyu.

Shugabar ta yi kira da a dauki matakin gaggawa domin karfafa tsarin tallafawa mata masu shayarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: