Gwamnatin Jihar Gombe ta kaddamar da wata na’urar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai karfin kilowat 620 a madatsar ruwa ta Balanga da ke garin Talasse a karamar hukumar Balanga a jihar.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwa gwamnan Jihar Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana aikin a matsayin wani babban ci gaba a yunkurin da jihar ke yi na samar da makamashi, samar da wutar lantarki a yankunan karkara da bunkasa masana’antu.

Gwamna Yahaya wanda mataimakinsa Dokta Manassah Daniel Jatau ya wakilta, ya jaddada cewa kaddamar da shirin ya yi daidai da babban alkawurran gwamnatin Jihar na samar da ababen more rayuwa, da karfafa tattalin arziki da dorewar muhalli a fadin Jihar.

Gwamnan ya ce samar da wutar lantarki zai kawo sauyi ga rayuwar al’ummar Jihar, da hanyar kara kaimi wajen yin noma, da samar da ayyukan yi a Balanga da sauran yankunan Jihar.

Gwamna Yahaya ya kuma mika godiyarsa ga al’ummar karamar hukumar ta Balanga bisa goyon bayan da suka bayar wajen yin aikin.,

Leave a Reply

%d bloggers like this: