Ministan yada labarai Mohammed Idris ya bayyana cewa za su tabbatar da ganin sun sasanta tsakanin gwamnatin Jihar Neja da gidan rediyon Badeggi da gwamnatin Jihar ta rufe.

Ministan ya bayyana hakan ne a yau Asabar ta cikin wata sanarwa, yana mai cewa dakatar da lasisin kafar yafa labaran ya rataya ne a wuyan hukumar yada labarai ta kasa NBC.

Sanarwar ta yabawa gwamnatin jihar ta Neja kan matakin da ta dauka na kai rahoto a hukumance kan rufe shi.

Ministan, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu domin hukumar NBC na daukar matakan da suka dace don warware matsalar cikin adalci.

Gwamna Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon ne tare da kwace lasisin sa bisa zargin yada labaran da bana gaskiya ba.

Rufe gidan rediyon na ci gaba da haifar da suka ga gwamnatin Jihar ta Neja kan daukar matakin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: