Shugaban kasar Ghana John Mahama ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen kare rayuka da lafiyar ‘yan Najeriya da kuma kasuwancinsu a kasar.

Shugaban Ƙasar ta Ghana ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin karamar ministar harkokin wajen Najeriya Bianca Odumegwu-Ojukwu a fadarsa da ke Accra.

A wata sanarwa mai dauke da sanya hannun mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na ofishin karamar ministan Magnus Eze ya fitar jiya Juma’a, Mahama ya bukaci shugaban Kasa Bola Tinubu da ya kara kaimi wajen ci gaban ƴan Kasarsa.

Shugaban na Ghana ya kuma tabbatar da cewa zai bayar da ingantaccen tsaro da kare rayuka, dukiyoyi, da kasuwancin ‘yan Najeriya a Kasar ta Ghana.

A yayin ziyarar Karamar Ministar ta godewa shugaban na Ghana bisa jajircewarsa wajen kulawa da ƴan Najeriya mazauna Kasarsa.

Ziyarar Ministar na zuwa ne biyo bayan wani faifan bidiyo da ake yadawa ƴan cin zarafin ƴan Najeriya a Kasar na Ghana, ta ce za su kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Ghana, tare da bukatar ‘yan Najeriya mazauna Ghana da su bi dokokin Kasar ta Ghana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: