Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa sun kama masu aikata laifi da dama ciki har da masu ɓarnartar da kayan gwamnati.

 

Kakakim ƴan sanda a jihar Lawan Shi’isu Adam ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

 

Ya ce an kama masu ƙwacen babur mai ƙafa uku, wanda ya haɗa da wata mace mai shekara 21 da wani Nazifi Ahmed.

 

Haka kuma akwai dillalan miyagun kwayoyi bamwai da aka kama tare da kayan maye da kuma makamai.

 

Jami’an sun ce sun kama kayan maye mai tarin yawa da kuma masu laifi da su ke sa ran gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

 

Kakakim ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an ci gaba da aikin tabbatar da tsaro a jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: