Hukumar Hisbah a Kano ta tabbatar da kama wasu mutane 26.

An kama mutanen a wani otel mai suna Grace Palace a kusa da barikin sojoji ta Bokabo a Kano.
Mataimakin kwamandan hukumar Sheik Muhadidden Aminudden ne tabbatar da haka a wata sanarwa da ya aikewa da Matashiya TV.

Ya ce an kama mutanen bayan samun ƙorafin al’umma a kansu.

Jami’an sun kuma kwaso giya da su ka tarar ana sha a wajen.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai maza 12 sai mata 14.
Hukumar ta buƙaci al’umma da su dinga sanar mata da zarar sun ga ana aikata wani abu da ya saɓawa shari’ar Muslunci.
