Jami’an sojin Operation Hadin Kai sun hallaja ‘yan ta’addar boko Haram 17, a wani samame da suka kai a jihohin Borno da Adamawa.

Mai magana da yawun rundunar Captain Reuben Kovangiya ya ce ‘yan ta’addan na kai hare-hare ne a kananan hukumomin Bama, Konduga, Gwoza, Magumeri, da Biu a jihar Borno, yayin da kuma suke kai hare-hare a Michika dake jihar Adamawa.
Ya ce sojojin sun kuma gano tare da kwance bama-bamai sama da 14 da ‘yan ta’addan suka binne a wurare daban-daban.

Acewarsa an samu nasarar ne hadin gwiwa da jami’an sojin sama, a ayyukan da suke gudanarwa a yankin Arewa maso gabas a ranar 23 ga Yuli zuwa 2 ga watan nan na Agusta.

Bugu da kari ya ce an kwato makamai da harsasai daga hannunsu, da suka hada da bindiga kirar AK-47 da dama, da bindigar PKT, harsasai da sauran kayan aikata ta’addacin.
Sannan an kuma kwato akalla lita 2,300 na Gas, da fiye da lita 1,000 na fitur da janareta biyu, babura uku, buhunan shinkafa, da dai sauransu.
