Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da akalla mutane 20 a Jihar Zamfara.

Wadanda masu garkuwar suka sace mafiya yawa ‘yan mata ne da mata a garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi ta Jihar.
Wani mazaunin garin Moriki mai suna Sufyanu Moriki ya shaidawa Channels TV cewa an sace mutanen ne a ranar Asabar din da ta gabata a lokacin da suke dibar itace a wajen garin.

Sufyan ya ce tun bayan sace mutanen har yanzu masu garkuwa ba su kira ba domin neman kudin fansa kafin sakin su.

Tun bayan lamarin har yanzu rundunar ‘yan sandan Juhar ba ta tabbatar da lamarin ba.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Yazid Abubakar ya ce bayan samun rahoton lamarin zai yi cikakken bayani akai.
