Jam’iyyar PDP a jihar Ogun ta nuna goyon bayan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu don sake zarcewa wa’adi na biyu.

Shugaban jam’iyyar a jihar ne ya bayyana haka yayin taron yaƙin neman zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Remo a jihar.

A cewarsa sun goyi bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake zarcewa wa’adi na biyu a zaɓen 2027 da ke tafe.

Ya ce shugaba Tinubu ba zai taɓa yarda da satar akwatin zaɓe ko yin maguɗi ba.

Wannan dai na zuwa ne yayin da wasu daga cikin jam’iyyar PDP ke ficewa tare da komawa jam’iyyar ADC a wani bangaren kuma wasu ke komawa cikin jam’iyya mai mulki ta APC.

Shugaban jam’iyyar ya yi kira ga al’ummar jihar da su fito don zaben dan takararsu na jam’iyyar PDP.

Hukumar zabe ta INEC a Najeriya ce dai ta sanar da zaben coke gurbi da za a yi na kujerun da yan majalisa su ka rasu a ranar 16 ga watan Agusta da mu ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: