Hukumar kula da yanayi ta Kasa NiMet ta ce Jihohin Gombe, Kano, Bauchi, da kuma jihohin Arewa bakwai za su fuskanci ruwan sama cikin kwanaki masu zuwa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a hasashenta na watan Agusta, da ta fitar a yauTalata a Gombe.
A cewar hukumar sauran Jihohin da za su fuskanci ruwan sun hada da Sokoto, Zamfara, Jigawa, Katsina, Yobe, Borno, da Kebbi.

Hukumar ta ce watan Agusta za a samu karuwar ruwan sama da kuma yawan ruwa, musamman a yankunan Arewa.

NiMet ta kara da cewa lamarin na iya haifar da cikar kogi, da ka iya haifar da ambaliyar ruwa.
Hukumar ta bukaci guraren da ke fama da ambaliyar ruwa da kogi da su kasance cikin shiri, tare da ficewa daga gidajensu.
Hukumar ta kuma bukaci shugabannin al’umma da su kara wayar da kan mutane kan yadda za su shawo kan ambaliyar da tsafta, da kuma daukar matakn kariya daga kamuwa da cutuka.
