Ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike ya ce za a dauki matakin rufe wasu gine-gin a Abuja wadanda har yanzu ba su biya kudaden harajinsu ba.

Wike ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a Abuja.

Ya nuna rashin jin dadinsa da cewa, duk da wa’adin da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar, wasu daga cikin masu gidajen sun ki biyan harajin.

Ya ce daga yanzu gwamnati ba za ta bar masu kadarorin ba su hana harajin da ake bin su.

Wike ya ce a baya sun bai’wa masu kadarorin wa’adin makwanni 14, inda wasu suka biya, yayin da har yanzu wasu suka gaza biya.

Acewarsa nan bada dadewa ba za su dauki matakin rufe kadarorin da ba su biya harajin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: