CSP Bala Mohammed jami’in ɗan sanda ɗaya tilo da ka iya zama madubi, ba ga ƴan sanda ba kawai har ma da al’umma baki ɗaya.

 

Ɗan sandan da ba ya karɓar cin hanci, mai gudun haram da taka tsan-tsan.

 

A halin yanzu shi ne baturen ƴan sanda da ke unguwar Hotoro a ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano, wani abin ban sha’awa a kansa, yayin da mutane ke gudun wasu jami’an ƴan sanda, Bala Mohammed mutane rububin raɓarsa su ke yi saboda kyautatawa da yake musu da kyawawan halayensa.

 

A ranar Litinin 11 ga watan Agustan shekarar 2025 da msialin ƙarfe 5:30pm na yamma wani al’amari ya kai ni ofishin ƴan sanda da ke unguwar Hotoro, da shigata kai tsaye na ga baturen ƴan sandan a bakin ƙofar shiga babbar harabar chaji ofis ɗin, nan take na sanar masa da cewar wajensa na zo.

 

Kai tsaye ya tashi mu ka nufi ofishinsa ba tare da na sanar da shi wanene ni ba, ban kuma bayyana masa dalilin zuwa wajensa ba.

 

Mu na shiga ofishinsa cikin tarba da karramawa da mutuntawa, ganin yadda ya karɓeni ban ɓata lokaci ba kai tsaye na gabatar masa da wanene ni da kuma abinda ke tafe da ni.

 

Daga kalamansa na fahimci mutum ne kaifi ɗaya, ma’ana abinda yake furtawa a baki har a zuciyarsa haka yake.

 

Ba tare da ɓata lokaci ba mu ka kammala na tafi saboda dare ya yi kuma ina da wani abin da na bari a wajen aiki nake so na je don na kammala.

 

Washegari ranar Talata 12 ga watan Agustan 2025, na koma don mu ƙarasa abinda ya kaini a ranar Litinin, nan ma ya karɓeni fiye da tarbar farko, ko da dai a karon farko bai iya ganeni ba saboda shigar da ya ganni da farko ba ita ya ganni a haɗuwa ta biyu ba.

 

Bayan mun kammala abinda ya kai ni a ranar, na fito kenan wajen ƙarfe 12pm na rana ta ɗan wuce, sai na tarar an shigo da wani ƙaton mazubin abinci (Cooler) ban tambayi menene ba, ban kuma tsaya bibiya ba saboda ba wannan ne ya kai ni ba, a nan dai na tafi abuna.

 

Na sake komawa ofishin ƴan sandan a ranar Litinin 18 ga watan Agustan shekarar 2025, a wannan rana na shafe aƙalla sa’a guda tare da shi.

 

Da fitowata daga ofishinsa, yayin da ya rakoni, sai na sake riskar an sake kawo wannan ƙaton mazubin abincin (cooler) sai ya tsaya ni ma na tsaya, ashe abinci ne dafaffe a cikinta.

 

Dafaffe ne cikin tsafta, nan da nan na ga ana ta shigo da kwanuka da robobi na zuba abinci, tun daga jami’an ƴan sanda da mutanen gari, almajirai da marasa ƙarfi.

 

Da farko ya fara umartar a fara zubawa mutanen da ke rufe/tsare da su a ɗakin ajiya (suspects) sannan aka ci gaba da zubawa jami’an ƴan sandan da ke ƙarƙashinsa da kuma mutane marasa ƙarfi farar hula da almajirai.

 

Ban taɓa ganin ofishin ƴan sanda da mutum ke rububin zuwa kamar inda na tarar da Bala Mohammed ke shugabantar wajen ba wato ofishin ƴan sanda na Hotoro.

 

Ba wannan ne kaɗai abin birgewa ba, CSP Bala Mohammed a mu’amalarsa da abokan aikinsa ƴan sanda ba za ka ce shi ne babba ba, saboda yadda su ke wasa da dariya da kuma haba-haba da jama’a.

 

Kaancewarsa shi ne shugaba, ya sauya dukkan alƙiblar na kasa da shi abokan aikinsa ƴan sanda a wurin da yake aiki.

 

Ba wannan ba, yadda jami’an ke ƙoƙarin gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa zai tabbatar maka da cewa ya samo asali ne daga shugabancin da su ka samu na CSP Bala Mohammed.

 

Aikin ake yi cikin ƙwarewa ba tare da cin mutunci ko zarafin wanda ake zargi da ma sauran al’umma ba.

 

Wanene Bala Mohammed?

CSP Bala Mohammed ɗan asalin Nguru ne a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya fara aikin ɗan sanda a shekarar 2005, kuma ya fara da muƙamin mataimakin sufurtandan ƴan sanda wato (ASP).

 

Ya yi aiki a wurare da dama cikin jihohin Borno, Bauchi da Kano.

 

A Kano ya zauna a a helkwatar ƴan sanda, Gwagwarwa, Ƙofar Wambai da Hotoro da yake a halin yanzu, da sauran wurare.

 

Ko da na yi imanin cewar ba shi kaɗai ne ɗan sanda na gari ba, amma shi na sani, kuma idan ana son karramawa bisa cancanta ba don suna ko alaƙa da sanayya ba, tabbatar CSP Bala Mohammed ya cancanci kowacce irin karramawa.

 

Halayyarsa ta nuna cewar ya samu tarbiyya daga iyaye na ƙwarai, kuma ya samu ilimi na addinin musulunci da kuma ƙoƙarin kwatanta aiki da shi, irinta ake so shugabanni su kasance su na da ita, daga ciki akwai taka tsan-tsan, gudun haram da ƙoƙarin tabbatar da adalci.

 

Da mafi yawan ƴan sanda za su zama kamar Bala Mohammed ko ma fiye, da sun ci gaba da amsa sunan ƊAN SANDA ABOKIN KOWA.

 

Kafin na yi wannan rubutu na yi bibiya ga waɗanda su ka sanshi kuma su ka yi mu’amala da shi, abinda kowa ke faɗa bai wuce kyawawan halayensa ba.

 

Tsawon shekara 20 ya shafe ya na wannan aiki a Najeriya, tabbas ya bayar da gudunmawa musamman yadda ya tsare aikin da mutuncinsa.

 

Zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga shugabanni a matakin jiha, tarayya har ma da majalisar ɗinkin duniya don ganin an ƙarfafi irin kyawawan halayensa ko sauran ƴan sanda za su yi koyi.

 

Ba karramawa kaɗai ba, a yi masa abinda zai zama kwatance da hujja, domin tabbatar da makomar wanda ya tsare mutuncinsa da aikinsa.

 

A ɓangaren aikinsa, ya kamata hukumar ƴan sanda ta ƙasa ta yi wani abu da za ta fito da CSP Bala Mohammed da ire-irensa, don tabbatarwa da duniya ta na goyon bayan aikin ɗan sanda mai tsafta, gaskiya, adalci da tabbatar da doka, domin halayyar da yake nunawa ba kansa kaɗai ba har hukumar ma ya tsare mata nata mutuncin.

 

Al’ummar Najeriya ma ya kamata su yi duk wani abu da za su ƙarfafa masa gwiwa.

 

Tabbas mutane ba za su so su yi nesa da irinsu CSP Bala Mohammed ba.

 

Abubakar Murtala Ibrahim

(Abbanmatashiya)

Marubuci ne kuma ɗan jarida mai binciken ƙwaƙwaf

Shugaba kuma mamallakin kafar yaɗa labarai ta Matashiya TV da rediyo

Daga Kano a arewacin Najeriya

Abumurib1993@gmail.com

+2348030840149

Leave a Reply

%d bloggers like this: