Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar lll ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar tsaro da ake fuskanta a ƙasar.

 

A gefe guda kuma sarkin ya yabawa shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da ya ɗauka da ya sa kayan abinci ya karye a ƙasar.

 

Sarkin ya bayyana haka ne yayin jawabinsa a wajen taron wayar da kai da aka shirya kan nasarorin shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ma’aikatar yaɗa labarai ta ƙasa ta shirya jiya Alhamis.

 

Sai dai ya ce mutane da dama na rayuwa cikin tsoro da firgici sakamakon rashin tsaro da ake fuskanta a ƙasar.

 

A dangane da hakan ne sarkin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da ake yi a ƙasar na kisan kai da garkuwa da mutane.

 

A cewarsa su na bukatar ganin jama’a na rayuwa a gidajenau ba tare da firgici ba, sannan su je duk inda su ke so ba tare da wata fargaba ba.

 

Sarkin musulmi wanda sarkin Yakin Gagi Umar Sani ya wakilceshi, ya kuma yabawa tsarin bai wa ɗalibai rance da lamunin karatu wanda ya taimakawa ɗaliban manyan makarantu a ƙasa.

 

A cewarsa sun duba tsarin a hankali kuma sun fahimci cigaban da hakan ya kawo da kuma nasara a ɓangaren ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: