Gwamnatin jihar Imo ta sanar da haramta duk wani nau’i na hakar ma’adinai a cikin Owerri babban birnin Jihar nan take.

Gwamnatin jihar ta bayar da misali da yadda ake lalata muhalli, sakamakon hakar ma’adanan.

Kwamishinan ma’adanai na Jihar Ernest Ibejiako ne ya sanar da hakan, yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a fannin hakar ma’adanai da aka gudanar a Owerri.

Ya ce matakin ya biyo bayan shekaru da aka shafe ana hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi sanadiyyar mummunar ambaliyar ruwa, zaizayar kasa, da rushewar muhimman ababen more rayuwa a fadin birnin.

Ya ce a don haka gwamnatin Jihar ba za ta zuba idanu ba, a dunga ci gaba da hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Kwamishinan ya kuma bayyana jindadinsa ga ministan ma’adanai, bisa daukar mataki cikin gaggawa da yayi kan koken jihar ta hanyar tura tawagar manyan daraktocin tarayya domin tantance halin da ake ciki.

Ya ce gwamnatin gwamna Hope Uzodinma da ke aiki a karkashin sashe na 28 na dokar amfani da filaye ta shekarar 1978, ta sanar da gwamnatin tarayya a hukumance, tare da neman ta soke duk wani lasisin hakar ma’adinai a babban birnin Owerri.

A cewarsa duk da haramcin da aka sanya tun a shekarar 2017 da kuma karfafawa a shekarar 2019 da karamin ministan ma’adanai na wancan lokacin Uche Oga ya yi, an ci gaba da hakar ma’adanan ba bisa ka’ida ba, da kuma hakar yashi, lamarin da ya haifar da gurbacewar muhalli.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa gwamnatin Uzodinma na ci gaba da jajircewa wajen samar da ci gaba mai dorewa da kuma kiyaye gurɓacewar muhalli, yana mai jaddada cewa jihar za ta tallafa wa ayyukan hakar ma’adinai ne kawai a wajen babban birnin Jihar, tare da bin ka’idojin tantance tasirin muhalli, tsare-tsaren kula da muhalli da kuma yarjejeniyar ci gaban al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: