Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta Ƙasa FRSC reshen Jihar Borno, ta tabbatar da mutuwar mutane biyu, tare da jikkatar wasu Takwas a wani hatsarin mota da ya afku a Maiduguri babban birnin jihar.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, a lokacin da wata babbar mota ta afkawa motocin da ke tafiya a mahadar ‘yan sanda da ke Maiduguri.

Kwamandan hukumar a Jihar Usman A Muhammad, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya danganta lamarin da kwacewar birki.

Ya ce dukkan waɗanda ke cikin motar maza ne.

Ya kara da cewa an kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na Maiduguri, domin kula da lafiyarsu, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa na asibitin.

A cewar shaidun gani da ido, sun ce direban babbar motar ya ƙasa sarrafata, inda ya bugi wata mota da baburin adaidaita sahu, yayin da dukkan su na dauke ne da fasinjoji.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: