Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Ƙasa NDLEA ta kama daurikan hodar iblis da ake shirin fita da ita zuwa kasar birtaniya tare da wadanda ake zargi mutum shida.

Hukumar ta kuma ce ta tarwatsa wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi da hodar iblis guda shida a kokarin suke kokarin tafiya da ita kasar ta birtaniya.
Aikin wanda aka shafe tsawon makonni uku ana gudanar da shi a fadin jihar Legas, ne ya kai ga kama wasu mutane shida da ake zargi da su, ciki har da wani ɗan sarki da ake zargi, Alhaji Hammed Ode.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.

Ya ce an fara aikin sumamen ne a ranar 16 ga watan Satumba 2025, lokacin da jami’an hukumar da ke filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas, suka kama daurin hodar ibilis 174 mai nauyin kilogiram 13.4 da aka boye a cikin robar man shafawa na cocoa butter.
Ya ce wadanda aka kama sun boye kwayar ne a cikin kofuna, robar man shafawa, da kuma robar man gashi
Babafemi ya ce an kama wadanda suke safarar kayan manyan, kuma su na ci gaba da binciken bayan, da aka alakanta kayan da Ode, wanda daga baya aka kama shi tare da hadin gwiwar ‘yan sanda.
A cewarsa, a yayin da ake yi masa tambayoyi, Ode ya amsa cewa shi ne mai kwayoyin, inda ya ce ya siye su ne sama da Naira miliyan 150.
Kazalika Babafemi ya kara da cewa wadadnda ake zargi su biyu Ogunbiyi Taiwo da papola Olumuyiwa, an kama su bayan jami’an hukumar ta kama robar crayfish da kofunan da sukayi amfani da su wajen boye hodar iblis din da ya kai gram 2.6