Uwargidan Shugaban Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Sanata Oluremi Tinubu, ta bukaci a sake mayar da hankali kan magance matsalar karancin malamai a duniya.

Oluremi ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta sanyawa hannu a ranar Lahadi, a lokacin da ta ke taya murna da zagayowar ranar malamai ta duniya.

Uwargidan shugaban ta bayyana malamai a matsayin jarumai na gaske, masu sauya tunani, da kuma jagoranci.

Uwargidan shugaba Tinubu ta kuma amince da gagarumar rawar da malamai ke takawa wajen gina kasa da kuma makomar dan adam, inda yabawa malamai a fadin kasar nan.

Kazalika ta bayyana cewa ita kanta tana mutunta koyarwa da kuma wadanda suka sadaukar da rayuwarsu akanta.

A cewarta taken bikin na bana, shi ne Mayar da hankali kan Karancin Malamai a Duniya, kuma abin tunatarwa ne kan bukatar gaggawa na magance raguwar adadin malamai a duniya.

Har ila yau ta ce Karancin malamai kalubale ne da ya zama dole su fuskance shi cikin gaggawa, ta hanyar karfafawa malamai, saka hannun jari don bunkasar su, da kuma kara zaburar da su don shiga harkar koyarwa mai daraja.

Inda ta mika sakon gaisuwa ta musamman ga dukkan malamai a Najeriya, bisa zagayowar ranar da aka gudanar a yau Lahadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: