Jami’an sojin runduna ta shida ta ceto wasu fasinjoji shida da aka yi garkuwa da su ciki harda wani yaro a Jihar Taraba.

Jami’an sun samu nasarar ne ta cikin wani sumamen hadin gwiwa da su ka yi da jami’an ƴan sanda.
Mukaddashin daraktan yada labaran rundunar, Laftanar Umar Mohammed, ne ya bayyana hakan a garin Jalingo babban birnin jihar a jiya Asabar.

Ya ce wadanda ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da fasinjoji ne daga wata mota kirar Toyota da ta taso daga Katsina-Ala a jihar Benue, inda suka tilastawa direban motar tsayawa a wani shingen bincike da aka yi watsi da shi.

Ya ce bayan samun rahoton lamarin hadin gwiwar jami’an su ka yi gaggawar kai dauki, tare da kubtar mutanen ciki harda direban motar.
Ya ce sun haɗa wadanda abin ya shafa da iyalansu.
Kwamandan rundunar Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da gaggauta kai dauki da hadin kai tsakanin sojojin da ‘yan sanda suka yi, wanda ya kai ga samun nasarar.
Ya kuma kara jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Taraba.