Hukumar jindadi Alhazai ta Ƙasa NAHCON ta bayawa shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima bisa umarnin da suka bayar na rage farashin kudin aikin hajjin shekarar 2026, inda ta bayyana hakan a matsayin abin da ya dace da zai kawo sauki ga mmusamman ga aniyyata a fadin kasar nan.

Shugaban hukumar da daukacin ma’aikatan hukumar ta Najeriya, ne suka yabawa da matakin na shugaban Ƙasa da Mataimakinsa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar a yau Talata, ta ce hakan babban abin a yawa shugaban ne bisa namijin kokarinsa wajen ganin maniyyata sun samu damar gudanar aikin hajjin.

Hakazalika NAHCON ta yi kira ga gwamnatni da ta yi kira ga maniyyata da hukumomin jindadin Alhazai na Jihohi da su ci gajiyar shirin a halin yanzu ta hanyar tura kudadensu da wuri.

Acewar sanarwar umarnin yana ƙarfafa ci gaba da goyon bayan da shugaba Tinubu ke bayarwa don inganta harkokin aikin Hajji a Najeriya ta hanyar yin ayyukan da ke sanya aikin cikin sauki, gaskiya, da kuma daidaitawa.

Ta ce NAHCON za ta hada kai da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an aiwatar da umarni cikin gaggawa da kuma gudanar da aikin Hajjin bana na cikin sauki ga maniyyatan Najeriya.

Hukumar ta yi kira ga maniyyatan na 2026 da su gaggauta biyan kudadensu, domin bayyana sabon kudin kudin da za a sanar nan ba da jimawa ba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: