Mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ya bukaci yan Najeriya da su kare hannun jarin da Dangote ya zuba don amfana a nan gaba.

Shettima ya bayyana haka ne yau Litinin a wajen taron tattalin arziƙi da a ka yi a Abuja.
A cewarsa Dangote wani ginshiki ne na cigaban tattalin arzikin ƙasar.

Ya ce matatar mai ta Dangote da a ka kashe sama da dala biliyan 20, kadarar kasa ce da za ta habakara ta kuma sa a yi gogayya da ita a duniya.

Kalaman mataimakin shugaban na zuwa ne bayan da maaikatan man fetur da gas a Najeriya su ka tafi yajin aiki a makon da ya gabata.
Shettima ya bayyana Dangote a matsayin wata fitilar harkaka tattalin arzikin Najeriya.