Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni ga hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) da ta sake duba kudin kujerar aikin Hajji na shekara ta 2026 tare da rage shi, bisa ga ingantuwar darajar Naira a kasuwar musayar kudi.

A sakamakon wannan umarni, Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bai wa hukumar NAHCON wa’adin kwanaki biyu don fitar da sabon tsarin kudin kujerar aikin Hajji da zai dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar.

Shettima ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa, yayin taron da ya jagoranta tare da shugabannin NAHCON da wasu jami’an gwamnati, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jami’an jihohi da gwamnoni wajen tabbatar da sabon tsarin da ya dace.

Ya kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta biyan kuɗaɗen da suka wajaba da aika su ga Babban Bankin Najeriya (CBN) domin gudanar da aikin Hajji cikin nasara da tsari.

Da yake bayani ga manema labarai bayan taron, Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadeija, ya ce manufar taron ita ce kammala shirye-shiryen aikin Hajji na 2026, musamman batun kudin kujeru.

Ya ce, “Tun da darajar Naira ta samu ƙaruwa a kasuwa saboda gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ke yi, dole ne hakan ya bayyana a cikin kudin aikin Hajji. Idan masu aikin Hajji sun biya Naira Miliyan 8.5 zuwa Naira Miliyan 8.6 a bara saboda raguwar darajar Naira, yanzu da ta inganta, dole ne su amfana da saukin kudin.

Shi ma Sakataren NAHCON, Dr. Mustapha Mohammad, ya ce umarnin shugaban ƙasa zai ƙara yawan masu niyyar zuwa Hajji a bana.

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi, kuma Mataimakin Shugaban Kungiyar Shugabannin Hukumar Alhazai ta Jihohi da birnin tarayya, Alhaji Faruk Aliyu Yaro, ya bayyana farin cikinsa da wannan mataki.

Ya ce, “Muna murna sosai da wannan mataki da shugaban ƙasa da mataimakinsa suka ɗauka. Mun yi imanin hakan zai rage farashin kujerar Hajji kuma ya sauƙaƙa wa musulmi.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: