Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya danganta tsadar gas ɗin girki da yajin aikin da kungiyar ma’aikatan man fetur da gas su ka yi a makon jiya.

Shugaban kamfanin Bashir Bayo Ojulari ne ya bayyana haka.

Sannan ya zargi wasu daga cikin masu siyar da gas din da yin amfani da damar yajin aikin wajen ƙara farashinsa.

Ojulari ya bayyana haka a birnin Legas wanda ya ce da gangan a ka ƙirƙiri tsadar gas ɗin wanda a ka danganta da yajin aikin ƙungiyar ma’aikatan man fetur da gas ta Najeriya.

Shugaban ya ce tunda har ƙungiyar sun janye daga yajin aikin da su ka yi ya kamata a ce komai ya koma daidai farashin ya koma yadda yake.

A cewarsa, yajin aikin ya haifar da tsaiko wanda za a iya ɗaukar wani lokaci kafin komai ya koma daidai.

A makon jiya ne dai ƙungiyar ma’aikatan man fetur da gas a Najeriya su ka shiga yajin aiki bayan saɓani da su ka samu da matatar mai ta Dangote na korara wasu ma’aikata.

Sai dai sun janye bayan da gwamnatin tarayya ta shiga tsakani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: