Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa a wani gagarumin yaki da safarar miyagun kwayoyi, ta kama mutane akalla 105 a wani samame da suka kai a fadin jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Lawan Shi’isu Adam ne ya tabbatar da kama mutanen a ranar Talata a hedikwatar rundunar da ke Dutse babban birnin jihar.

Shisu ya bayyana cewa a wani sumame na baya-bayan nan jami’an rundunar sun gudanar da bincike a kowane lungu da sako na jihar domin kawar da miyagun kwayoyi.

A cewarsa, sumamen ya kai ga kwato miyagun kwayoyi sama da 5,000 da wasu kayayyaki masu alaka maye da suka hada da tabar wiwi da wasu magungunna daban-daban.

Ya ce daga cikin abubuwan da aka kama kwato sun hada da rukuni 2,541 na Exol da na D-5 guda 1,146, wadanda aka saba amfani da su a yankin.

Haka kuma sun kwato Tramadol 270 da tabar wiwi sama da dubu.

Sauran abubuwan da aka kama sun hada da Diaxer guda 269, da wasu kwayoyin 235, da sauran wasu kwayoyin.

Kazalika Kakakin ya bayyana cewa an kwato makudan kudade da suka kai Naira 92,460 daga hannun wadanda ake zargin.

Kakakin ya bukaci jama’a da su bai’wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar kai rahoton wasu abubuwan da ba su yadda da su ba.

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: