Gwamnan jihar Enugu Peter Mbah, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a hukumance.

Ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabi da ya yi ga al’ummar jihar.

Gwamnan ya kare matakin da ya dauka na sauya sheka, inda ya ce ya zama wajibi ya dauki matakin da ya dace domin hada yankin Kudu maso gabas da gwamnati.

Acewarsa bayan dogon tunani da nazari, ya ɗauki matakin komawa jam’iyyar APC.

A cewar Mbah, matakin da ya dauka na komawa jam’iyyar APC shi ne don kyautatawa mutanen Enugu da kuma yin daidai da manufofin jam’iyyar na ci gaba.

Gwamnan ya kuma jaddada aniyarsa na ciyar da muradun jihar gaba tare da bayyana kwarin gwiwar cewa tsarin jam’iyyar APC zai samar da damarmaki masu yawa na hadin gwiwa da ci gaba.

Mbah ya kuma yabawa manufofin shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa jihar ta samu gagarumin goyon baya a karkashin shugaban kasa.

Har ila yau gwamnan ya koma jam’iyya APC tare da ‘yan majalisar dokoki, kansiloli, shugabannin Kananan hukumomi, da dai sauran su.

A karshe Mbah wamnan ya godewa jam’iyyar PDP bisa goyon bayan da ta bashi tsawon shekaru, yana mai jaddada cewa sauyin ya zama wajibi don kara cimma manufofin gwamnatin sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: