Sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa Sanata Kaila Samaila ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

A cikin wata wasika da Kaila ya bai’wa shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, kuma aka karanta a zaman majalisar na yau Talata, ya bayyana rikicin da ya da baibaye jam’iyyar kuma aka gaza kawo karshensa ne babban dalilin da ya sanya ya sauya shekar.

Dan majalisar ya ce rikice-rikicen cikin gida da jam’iyyar ta PDP ke fama dashi ,ya yi matukar tauye masa damar yiwa mutanen da ya ke wakilta hidima yadda ya kamata.

Ya ce ya mayar da hankali ne wajen yi wa al’ummarsa hidima da kuma jin dadinsu, hakan ya sanya ya ga ya zama wajibi, ya daidaita harkokin siyasarsa, tare da ingantaccen tsarin ci gaba wanda ya kunshi shugabanci nagari, hadin kai, kuma ci gaba.

Kaila ya ce sauye-sauyen da shugaban kasa Bola Tinubu ke yi ne ya sa ya koma jam’iyyar APC mai mulki, wanda ya bayyana a matsayin kawo sauyi.

Sanatan ya kuma yabawa Akpabio bisa abin da ya bayyana a matsayin shugabanci abin koyi na majalisar dattawa ta goma.

A karshe Samaila ya yi alkawarin yin biyayya ga sabuwar jam’iyyarsa tare da jaddada kudurinsa na ganin an samu hadin kai da ci gaban kasa.

Da sauya shekar Kaila, jam’iyyar APC na da Sanatoci 74, PDP 27, Jam’iyyar Labour Party na da hudu, Jam’iyyar APGA na da biyu, NNPP na da daya, yayin da SDP ta ke da daya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: