Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya bayyana cewa babu wani alkali na babban birnin tarayya Abuja, da zai zauna a gidan haya a karshen wa’adin farko na shugaba Bola Tinubu.

Wike ya yi wannan alkawarin ne a wajen kaddamar da gina rukunin gidaje 40 na shugabannin kotuna da ke Abuja.

A wajen bikin, Ministan ya bayyana cewa, kudaden aikin na kunshe ne a cikin kasafin kudin 2024 da 2025 na babban birnin tarayya, kamar yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar, wanda majalisar tarayya ta amince da shi, kuma shugaban kasa ya amince da shi.

Wike ya kuma ce za a raba tsarin gidajen zuwa goma na alkalan kotun daukaka kara goma, na manyan kotunan tarayya goma, yayin da 20 kuma na alkalan babbar kotun tarayya na Abuja.

Ya bada tabbacin cewa shugaba Tinubu zai mika gidajen ga wadanda suka amfana bayan kammala wa’adin watanni 12 na aikin.

Idan ba a manta ba a baya Ministan na Abuja, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu zai magance kashi 80 cikin 100 na matsalolin gidaje da alkalai ke fuskanta a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: