
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Ibrahim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa; nan ba da jimawa ba, za a kawo karshen matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, a wani sabon mataki na bunkasa tattalin arzikin kasar.


Da yake jawabi, a yayin taron sabunta samar da makamashi a Nijeriya (NREIF) ranar Talata a Abuja, Shettima ya ce; zuciyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tare da ‘yan Nijeriya, sannan kuma yana sane da irin radadin da suke ji.
“Zuciyar shugaban, na matukar rashin jin dadi, dangane da radadin da ‘yan Nijeriya ke fama da shi, amma kuma muna bayar da tabbacin cewa; ana dab da samun saukin warwarewar al’amuran baki-daya.”
Mun samu labarin cewa, Hukumar Raya Wutar Lantarki ta Karkara (REA), ta shirya taron ne domin neman saka hannun jari, wajen samar da kayayyakin da ake sabuntawa a cikin gida.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa, taron goron gayyata ne na kafa Nijeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi tare da sabuntawa a Afirka, sannan kuma sauyin da aka samu na makamashi Nijeriya, ya bayar da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410, daga tsakanin yanzu zuwa shekarar 2060.
Ya kara da cewa, “Daga cikin wannan, ana kuma bukatar sama da Naira biliyan 23, domin fadada hanyoyin samar da makamashin da kuma hada miliyoyin ‘yan Nijeriya, wadanda har yanzu suke rayuwa cikin matsalar wutar lantarki, amma yanzu babban burinmu shi ne, samar da tsarin samar da wutar lantarki mai karfin mega wat 277, nan da shekarar 2060. Cikar wannan buri, ya wuce batun zuba hannun jari kadai, domin yana bukatar kirkire-kirkire, bayar da gudunmawa a cikin gida da kuma sadaukarwa.
“Wannan shi ne dalilin da yasa taken taron na bana ya kasance a matsayin, Aiwatar da Manufofin Nijeriya na Farko da Gudanar da Ci gaban Abubuwan Cikin Gida da kuma Samar da Makamashi, yana da matukar muhimmanci. Kazalika, yunkurinmu na dabarun masana’antu a Nijeriya na kira gare mu da mu dage kan makomar hanyoyin samar da makamashi na Afirka a nan gida.”
Ya kara da cewa, a karkashin wannan, an hada sama da dala miliyan 400 na sabbin alkawuran saka hannun jari a bangaren sabunta makamashi mai a Nijeriya.
A nasa bangaren, Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya ce; taron NRIP na 2025, ba wani taro ne da kawai aka shirya ba, sai dan shelanta cewa, Nijeriya a shirye take ta jagoranci sauye-sauyen makamashin da ake samu a Afirka.
Taken taron na bana shi ne, ‘Aiwatar da Manufofin Najeriya na Farko’, yana magana ne a kan wani abu mai mai muhimmanci da ya dara masana’antu, wanda ya kunshi jajircewa, kwarewar masana’antu da kuma dorewar tattalin arziki na tsawon lokaci.
“A bangaren samar da wutar lantarki, manufar Najeriya ta farko ta nuna aniyar tabbatar da cewa; zamani na gaba na fasahar samar da makamashi mai inganci, tun daga na’urori masu amfani da hasken rana har zuwa na’urorin adana makamashin batiri da aka baza a fadin kasar, na alfahari tare da dauke da lakabin, “Wanda aka samar a cikin gida Nijeriya’.”