Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP na kara matsa masa lamba kan ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Wike ya bayyana hakan ne ta hannun babban maitaimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Lere Olayinka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

Sanarwar ta bayyana rahotannin a matsayin na karya, daga wasu mutanen da ba sa son ci gaban Ƙasa.

Olayinka ya ce rahotanni da ake yadawa a shafukan yanar gizo wani yunkuri ne na haifarwa da Wike wata matsala.

Acewarsa an bayyana cewa a wani taro da wani taro da manyan jam’iyyar PDP suka gudanar ne suka matsawa ministan da ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027, inda ya ce hakan ba gaskiya ba ne, inda ya ce Wike na tare da Tinubu a 2027, kuma na yi masa fatan kai’wa 2031 akan mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: