Gwamnatin jihar Gombe ta kaddamar da bayar da tallafin Naira miliyan 726 ga dalibai mata 12,101 da suka fito daga kananan makarantun gwamnati da manyan makarantun sakandire a fadin jihar.

Tallafin wanda aka bayar a ranar Juma’a, inda aka bayar da tallafin da nufin inganta samar da ingantaccen ilimi ga yara mata masu tasowa da kuma inganta ababan more rayuwa a makarantu a fadin jihar.

Mataimakin gwamnan Jihar Manassah Daniel Jatau ya ce bayar da kuɗin, ta hanyar tallafin Inganta Makaranta sakandire na ‘yan mata, ya kasance ƙarƙashin Shirin AGILE na Koyo da Ƙarfafawa shirin tallafin Bankin Duniya.

Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne a gurin wani taro a matsayin wani mataki na ci gaban ilimi a jihar, ya kuma jaddada kudirin gwamnatin na samar da ingantaccen ilimi mai inganci ga kowa da kowa a dukkan fadin Jihar.

Acewarsa shirin ya shafi iya dalibai mata ne kawai, bisa tabbatar da juriyarsu, kulawa, da gudummawar da suke bayarwa ga ci gaban iyali da zamantakewa.

Jatau ya kuma sanar da bayar da wani tallafin ga makarantun sakandire na gwamnati 537 a fadin kananan hukumomin jihar 11, domin inganta ababen more rayuwa, tsaro, da kuma yanayin koyo, inda ya ce kasafta tallafin ne bisa duba da yawan daliban.

Ya ce kowacce na makarantun da ke da dalibai kusan 200 za ta samu Naira miliyan 23.1 , yayin da Naira miliyan 46.2 wadda ke da dalibai akalla 500 da kuma Naira miliyan 92.4 ga makarantun da ke da dalibai sama da 1,000.

Mataimakin gwamnan ya yabawa bankin duniya, da AGILE da ma’aikatar ilimi ta jihar, bisa jajircewarsu wajen samun nasarar shiri, sannan ya bukaci kwamitocin gudanarwa na al’umma gatan makaranta SBMC da sauran al’umma da su tabbatar da ganin abin hanoyin da suka kamata a yayin shirin.

Itama anata jawabin kwamishiniyar ilimi ta jihar Dr Aishatu Umar Maigari, ta ce kaddamar da shirin na a matsayin tarihi a gwamnatin gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na kawo sauyi ga ilimi, musamman a bangaren makarantun firamare da sakandare.

Ta yi kira ga kwamitin SBMC da su tabbatar da yin amfani da kudade ta hanyar da ta dace, tare da taya wadanda suka ci gajiyar tallafin karatu murna, inda ta bukace su da su mayar da hankali da jajircewa wajen karatunsu.

Anata bangaren Ko’odinetan ayyuka ta AGILE a jihar Dr Amina Haruna Abdul, ta bayyana cewa manufar shirin ita ce kawar da cikas ga ilimin ‘ya’ya mata ta hanyar bayar da tallafin kudi, inganta ababen more rayuwa, da kuma karfafa tsarin tafiyar da makarantu.

Ta ce tallafin karatu ya shafi dukkanin kananan hukumomin jihar 11, inda ta kara da cewa rukunin farko an tabbatar da an biya su, yayin da rukuni na biyu ke ake jiran tantancewa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: