Hukumar hana fasa kauri a Najeriya Kwastam a karkashin shirinta na tabbatar da tsaro na musamman, ta kama wasu manyan motoci biyu dauke da man fetur lita 120,000 da ake zargin an karkatar da zuwa wani guri na daban.

Acewar kodinetan hukumar na shiyyar B Kola Olawole, ya ce motocin kowannensu na dauke da lita 60,000 na man fetur, inda aka kama su a kan hanyar Sokoto zuwa Illela a ranar 4 ga watan Oktoba.
Ya ce motocin za su yi jigilar man ne zuwa Kano, amma suka karkatar da shi zuwa Jihar Sokoto.

A ganawarsa da manema labarai a Sokoto a jiya Juma’a, Olawole ya bayyana cewa direbobin manyan motocin, sun nufi Sokoto ne a lokacin da ‘yan sanda suka yi yunkurin kama su.

Ya ce a binciken da suka gudanar sun gano an karkatar da man fetur ne domin yin fasa kwaurinsa a kan iyakar Illela, wanda hakan ya sabawa doko bisa rashin samun izini, da sauran laifuka.
Ya jaddada cewa karkatar da man babbar barazana ce ga tattalin arziki, domin hakan na kawo cikas ga ci gaban kasa, samar da makamashi da kuma rayuwar al’umma baki daya.
Ya ce an mika motocin da aka kama a hannun ga ko’odinetan hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya shiyyar Sokoto da Kebbi Ali Ajimi.