Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a kan babbar hanyar Igarra zuwa Ibillo a karamar hukumar Akoko Edo a jihar.

Mai magana da yawun runduna ƴan sandan Jihar Moses Yamu ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin nan.
Ya ce nasarar ta samu ne bisa hadin gwiwar da jami’an suka yi wanda ya tilastawa masu garkuwar tsere da barin wadanda suka yi yunkurin sacewa zuwa cikin daji.

Yamu ya bayyana cewa an yi yunkurin yin garkuwar ne da wasu ‘yan kasuwa da ke dawowa daga Kasuwar Ibillo ne a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce da safiyar ranar Juma’ar ne, rundunar ta samu kiran gaggawa game da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke shirin sace mutane a kan babbar hanyar Igarra zuwa Ibillo.
Acewarsa bayan samun kiran gaggawa Baturen ƴan sandan Igarra ya aike da jami’an tsaro zuwa wurin, inda da zuwansu ƴan bindigar suka yi harbe-harbe, yayin da jami’an tsaron suka yi nasara a kansu.
Ya ce dukkan wadanda abin ya shafa an ceto su ba tare da sun samu rauni ba, yayin da ake ci gaba da gudanar da binceke a cikin daji don kama wadanda ake zargi da tserewa.