Gwamnatin Jihar Adamawa ta amince da naira miliyan 460 ga kwalejin noma kimiyya da fasaha ta jihar Adamawa da ke garin Ganye, domin tallafawa shirye-shiryen inganta ilimi.

Bayar da kudaden ya nuna yadda gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya jajirce wajen karfafa ilimin manyan makarantu da inganta ayyukan noma a jihar.
Kazalika kudaden za su taimakawa kwalejin wajen biyan bukatun Hukumar kula da fasaha ta Kasa NBTE, da inganta kayan aiki, kamar dakunan gwaje-gwaje, ajujuwa, inganta koyo da koyarwa, da kuma inganta bincike.

Shirin na kuma nufin tabbatar da cewa waɗanda suka kammala karatunsu sun kasance masu jajircewa a cikin ƙasa na haɓaka aikin noma da fasaha.

Hakazalika shirin ya sanya kwalejin ta Ganye a matsayin babbar cibiyar noma a Arewacin Najeriya kuma ya yi daidai da manyan manufofin jihar na bunkasa aikin noma na zamani, da karfafa matasa ta hanyar ilimin fasaha.