Shugaban kwamitin gudanarwa na babban taron jam’iyyar PDP na kasa da za a gudanar a watan Nuwamba mai kamawa, kuma gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya jagoranci mambobin kwamitin shirya taron na kasa zuwa tantance wasu ayyuka kai tsaye a wasu muhimman wurare a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Ziyarar ta shafi manyan wurare da suka hada da filin wasa na Lekan Salami, da zababbun tashoshin mota, da sauran muhimman wurare da aka ware domin gudanar da babban taron jam’iyyar PDP na kasa mai zuwa da za a gudanar a garin na Ibadan babban birnin Jihar ta Oyo.

Gwamna Fintiri da tawagarsa sun tantance matakin shirin jihar mai masaukin baki, inda suka mayar da hankali kan kayan aiki, masauki, tsare-tsare na tsaro, da sauran muhimman ababen more rayuwa da ake bukata domin gudanar da babban taron.

A jawabinsa Fintiri ya yabawa gwamnatin jihar Oyo bisa shirye-shiryenta da jajircewarta na ganin an gudanar da taron ba tare da wata tangarda ba.

Fintiri ya jaddada aniyar jam’iyyar PDP na gudanar da babban taronta na kasa cike da gaskiya, da kuma ingantaccen tsari wanda zai kara karfafa hadin kai da martabar dimkuradiyyar jam’iyyar.

Za dai a gudanar da taron ne a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba mai kamawa a garin na Ibadan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: