Hukumar kare fararen hula a Najeriya NSCDC ta gargadi mambobin kungiyar #FreeNnamdiKanuNow da su daina lalata muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa a babban birnin tarayya.

Kwamandan NSCDC a babban birnin tarayya Olusola Odumosu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar dangane da shirin da dan rajin kare hakkin bil’adama Omoyele Sowore ya shirya na gudanar da zanga-zanga a ranar litinin domin sako shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOB Nnamdi Kanu.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, inda ya ce hukumar ba za ta amince da duk wani nau’i na lalatawa ko sace-sace da sunan zanga-zangar ba.

A sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun mai magana da yawun ta Monica Ojobi ya sanya wa hannu, ta ce hukumar ta aike da jami’anta dukkan wuraren kadarorin gwamnati, tare da tabbatar da kare lafiyar mazauna Abuja kafin lokacin da kuma bayan zanga-zangar.

Ya ce dukkan wanda aka kama da niyyar aikata laifi, zai fuskanci hukunci daidai da doka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: