Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa ya kai 172 a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa a ranar Talatar nan.
Rahoton baya-bayan nan da NCDC ta fitar ya ce ya zuwa mako na 40 a 2025, adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai kashi 18.6 cikin 100, daga kashi 17.0 da aka samu a daidai wannan lokacin a shekarar 2024.

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, zazzabin Lassa cuta ce mai saurin kamuwa, inda ta ce mutane na kamuwa da cutar ne ta hanyar beraye.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasashen da ke fama da zazzabin Lassa sun hada da kasashen Benin, Ghana, Guinea, Laberiya, Mali, Saliyo, Togo da Najeriya, inda ake kyautata zagon samunta a sauran kasashen yammacin Afirka.
Ya zuwa mako na 40, Najeriya ta samu adadin mutane 924 da aka tabbatar sun kamu da cutar, inda shekarar 2025, jihohi 21 sun samu rahoton kamuwa da cutar a cikin ƙananan hukumomi 106.
Acewar NCDC kashi 90 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar kashi 35 na a Ondo, kashi 22 Bauchi, Edo kashi 17, Taraba kashi 13, Ebonyi kashi 3, yayin da sauran kashi 10 cikin 100 na a wasu jihohi 16.
NCDC ta mafiya yawan wadanda suka fi kamuwa da cutar masu shekaru 21 ne zuwa 30.
Ta ce rohoton ya bayyana cewa babu wani ma’aikacin kiwon lafiya da ya shafa a cikin, kuma adadin wadanda ake zargi da tabbatar da kamuwa da cutar ya ragu idan aka kwatanta da lokaci guda a cikin 2024.