Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Dr Aminu Yusuf a matsayin shugaban hukumar kidaya ta kasa NPC, tare da wasu mutane biyu da aka tantance a matsayin kwamishinoni na tarayya.

Majalisar ta amince da nadin nasu ne biyo bayan gabatar da rahoton da kwamitin majalisar mai kula da al’amuran kasa da yawan al’umma ya yi a yayin zaman majalisar.
Da yake gabatar da rahoton a ranar Talata Sanata Victor Umeh Sanata mai wakiltar mazabar Anambra ta tsakiya, wanda ke jagorantar kwamitin, ya bayyana sunayen wadanda aka zaba a matsayin shugaban kwamitin da suka hada da Aminu Yusuf daga jihar Neja, da Joseph Haruna Kigbu daga jihar Nasarawa, da Tonga Betara Bularafa daga jihar Yobe a matsayin kwamishinonin.

Umeh ya ce kwamitin ne ya tantance wadanda aka nada, bayan sun bayyana a gaban kwamitin domin tantancesu a ranar 14 ga Oktoban nan.

Kwamitin bai samu korafe-korafen aikata laifuka a kan wadanda aka nada ba, inda suka shirya tsaf domin ci gaba da gudanar da aikin da aka tsayar.
Umeh ya bayyana cewa kafin tantancesu sai da kwamitin ya bukaci da su gabatar masa da takardun karatu, takardar shaidar tabbatar da aiki, rahoton ‘yan sanda, da kuma izinin daga DSS, kafin fara tantancewar.
Ya kara da cewa an fara tantancesu ta hanyar gabatar da jawabai daga kowane, tare da yi musu tambayoyi, inda daga ƙarshe kwamitin ya amince da su.
Bayan kammala tantancewar shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio, ya bayar da umarnin kaɗa kuri’a, inda ‘yan majalisar suka amince da nadinsu.
