Hukumar hana afkuwar haddura a Najeriya FRSC ta ce an samu raguwa haddura da kaso 6 a jihar Zamfara.

Kwamandan hukumar Aliyu Ma’aji ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da ya jagoranta a Gusau babban birnin jihar.
A cewarsa a shekarar 2025 an samu haddura 46 ƙasa da haddura 56 da a ka samu a shekarar 2024.

Ragin kaso 6.27 kenan la’akari da shekarar da ta gabata.

A cewarsa a shekarar 2024 an rasa rayuka 51 mutane 259 su ka jikkata, kuma su ke zargin daukar kaya da dabbobi da mutane wuri guda ne ya haddasa hakan.
Ya ce a halin yanzu sun ɗauki aniyar wayar da kai domin daƙile afkuwar hakan tare da tabbatar da bin doka da oda.
Kwamandan ya bukaci direbobi da ke bin manyan tituna da su kaucewa daukar kayan da du ka zarce ka’ida, da gwamutsa mutane da dabbobi da kaya wuri guda.
Idan za a iya tunawa, hukumar a Najeriya ta ce daga watan Janairu zuwa Satumban shekarar da mu ke ciki an samu asarar rayuka 3,400 sanadin tukin ganganci a Najeriya.
A cewar sanarwar da hukumar ta ƙasa ta fitar, mutane 22,162 ne su ka jikkata a tsakanin watannin
Sannan an samu haddura guda 6,858.