Ahmad Sulaiman Abdullahi

Hatsabibi kuma gagararren shugaban ƙungiyoyin ta’addancin da suka addabi yankunan jihohin Benue, Nasarawa da Taraba, Leggi Jibrin, ya shiga hannun jami’an tsaro bayan artabun musayar wuta da yayi da dakarun sojin rundunar Operation Whirl Stroke, rundunar tsaro ta haɗin gwiwa dake kula da jihohin uku.

Rahotanni daga bakin majiyar tsaro, sun bayyana cewa ɗan bindigan da OPWS ta daɗe tana nema ya shiga hannun sojoji ne a kauyen Agam, Gidan Bawa dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa yayin da suka fita aiki.

An samu nasarar ceto mutum 5 daga sansanin ƴan bindiga da ke dajin Zaure bayan samamen da zaƙaƙuran dakarun suka kai.

Majiyar ta ce dakarun sun yi aikin ne a ranakun Laraba da Alhamis karkashin umarnin kwamandan rundunar, Manjo Janar Kevin Aligbe.

Hakan yayi sanadiyyar ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su a Ugya dake karamar hukumar Toto ta jihar.

Kamar yadda majiya daga dakarun ta bayyana, “Sojojin OPWS da aka tura Ugya dake karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa sun samu gamsassun bayanai kuma suka hanzarta kai ɗauki bayan samu kiran da suka yi kan cewa an yi garkuwa da wasu mutane kuma an kai su dajin Zaure.

Daga isar su dajin, dakarun sun tarar da manyan motoci uku dankare da timber wacce aka ɗiba ba bisa ka’ida ba kuma aka bar su a dajin.

Kamar yadda dakarun suka ce, sun bincike dajin inda suka ci karo da sansanin masu garkuwa kuma suka ceto mutanen biyar.

“Wadanda aka ceto su ne Abdulkafar Nuhu, Adamu Dagana, Emmanuel Osased, Jacob Amaku da Danladi Amaku.

“A yayin aikin, dakarun sun cafke hatsabibin mai garkuwa da mutane a kauyen Agam/Gidan Bawa dake karamar hukumar Nasarawa a
jihar Nasarawa.

Ƴan bindigan suna tsaka da kai farmaki yankin yayin da OPWS suka dakile su.

An yi ruwan wuta tsakaninsu da dakarun wanda yayi sanadin kama Jibrin tare da halaka daya daga cikin ƴan bindigan.

“A yayin da jami’an mu suka shiga yankin da suka kai farmaki, wasu daga cikin ƴan bindigan ɗauke da miyagun makamai sun tsere yayin da suka hango jami’an.

“Daga nan dakarunmu suka fatattakesu inda suka yi musayar wuta.

Hatsabibin, wanda aka harba a kafa ya shiga hannun mu kuma wasu sun sheka lahira.

“Dole ne in ce an samu nasarar samamen nan ne sakamakon bayanan sirri da muka samu kan cewa hatsabibin tare da mukarrabansu sun kai hari wasu kauyukan yankin.”

Ya ce wasu daga cikin abubuwan da aka samu daga ƴan bindigan sun haɗa da bindiga kirar AK-47 daya, AK-49 daya, harsasai masu rai 106 tare da wayar tafi da gidanka.

Munyi Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun OPWS, Flying Officer Audu Katty amma hakan ya gagara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: