Ahmad Sulaiman Abdullahi


Alamu na nuni da cewa watakila gwamnatin tarayya ta aiwatar da manufar ba aiki, ba albashi domin daƙile yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta daɗe tana yi.

Matakin da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan sanarwa da wasu wasiƙu da hukumar da ke yajin aikin ta aikewa da wasu ƙungiyoyin jami’o’in da suka haɗa da kwamitin haɗin gwiwa na JAC wanda ya kunshi NASU da SSANU.
Shugaban ƙungiyar malaman jami’a ta NAAT, Ibeji Nwokoma ne ya bayyana wannan zargi kan gwamnatin tarayya.
Nwokoma ya tabbatar da cewa ba a biya ƴaƴan ƙungiyarsa cikakken albashinsu na watan Maris da gwamnati ta biya kwananan ba.
Majiyoyin da suka yi magana kan lamarin sun ce gwamnatin Najeriya ta yi amfani da manufar tsayar da albashin ne a watan Maris din 2022.
Nwokoma ya kuma zargi gwamnatin tarayya da yin watsi da duk wasu takardu da wasiku da aka aika na neman magance matsalolin da ƙungiyar da ta bijiro dasu.
A cewar Nwokoma, maimakon gwamnatin Najeriya ta gayyaci ma’aikatan da ke yajin aikin domin tattaunawa a kan lamarin, sai kawai ta aiwatar da manufofinta na ba aiki, ba albashi.
Ya kuma kara da cewa mambobin ƙungiyar ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen neman ingantaccen yanayin aiki ga ma’aikata da ɗalibai ba.
A cewar Nwokoma:
“Yau, mun shiga mako na biyar na yajin aikin gargaɗi, makwanni biyu na farko, sannan muka kwashe makwanni hudu.
“Abin takaici, kamar yadda muke magana, gwamnati ba ta kula da duk sanarwar yajin aikin ba da duk wasikun da muka rubuta musu har yau.
“Har ila yau, gwamnati ba ta gayyace mu ba, ko kuma ta ga ya dace ta gayyace mu wajen tattaunawa a kan teburi, domin a samo mafita ba.
“Kuma abin takaici, sai kawai gwamnati ta yanke shawarar dakatar da albashin mu, ta hanyar amfani da tsarin ba aiki, ba albashi.”