Ministan ruwa, Injinya Suleiman Adamu ya bayyana cewa
jihohi 32 da birnin tarayya Abuja zasu fuskanci ambaliyar ruwan sama a bana.

Jihohin daya lissafa zasu fuskanci ambaliya mai munin gaske a cewarsa sun haɗa da Lagos, Edo, Delta, Delta, Akwa Ibom, Abia da birnin tarayya Abuja.

A jihar Rivers, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo, Lagos, Ogun da Imo, ya ce za’ayi ambaliya ne saboda tekunansu sun cika kuma hakan zai shafi harkar masunta.

Ministan ya lissafa waɗannan jihohi a taron gabatar da rahoton hasashen ambaliya na shekara-shekara na hukumar ayyukan ruwa a Najeriya (NIHSA).

Ya bayyana cewa ƙananan hukumomi 233 zasu fuskanci ambaliya mai tsanani yayinda kananan hukumomi 212 zasu fuskanci ambaliya mara tsanani a bana.

Ministan ya ƙara da cewa ƙananan hukumomi 57 zasu fuskanci nasu ambaliyar tsakanin watan Afrilu da Yuni, yayinda sauran 220 zasu fuskanci nasu tsakanin Yuli da Satumba.

Cikin biranen da zasu fuskanci wannan ambaliya bana a cewarsa sune Lagos, Kaduna, Suleja, Gombe, Asaba, Port Harcourt, Benin da Lokoja.

A bara, Ministan ya yi hasashen mumunan ambaliyar ruwan sama a jihohin Najeriya akalla 28.

Jihohin da aka lissafo a bara sune,Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, FCT, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano and Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba da Zamfara.

Ministan ya ce saboda haka suka shirya don ankarar da ƴan Najeriya kan abinda ka iya faruwa.

Ya yi kira ga ƴan Najeriya su taimakawa waɗanda wannan iftila’i ya faɗama wa

Leave a Reply

%d bloggers like this: