Hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa da cin hanci a Najeriya ta na bincike a kan jam’iyyun PDP da APC ana tuhumar APC mai mulki da PDP mai hamayya a kan zargin wawurar kuɗi ta wasu bankuna.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta na binciken wasu kuɗi da suka shiga asusun PDP da APC.
Shugaban sashen gudanarwa na hukumar EFCC ta ƙasa, Michael Wetkas ya aika takarda zuwa ga shugabannin wasu manyan bankuna biyu da su ke Abuja.

Waɗannan wasiku sun shigo hannun ƴan jarida, inda aka fahimci jami’in hukumar ya sanar da bankunan cewa ana binciken kuɗin da suka shigo masu.

EFCC ta sanar da bankunan cewa akwai wasu akawun 14 da ake bincike a kansu, akawun ɗin na jam’iyyun siyasar ne da wani kamfani mai alaƙa da PDP.
Kamar yadda rahoton ya bayyan akawun uku da aka samu daga ɗaya daga cikin bankunan na jam’iyyar APC ne; 0692988080, 0035644896 da kuma 0044183689.
Akwai wani akawun mai lamba 0054586830, wanda sakatariyar jam’iyyar PDP ta mallaka.
cikin wasiƙar da Wetkas da ya aika, ya bayyana cewa ana binciken wasu asusu da APC ta buɗe a wani fitaccen banki; 0692988080, 0035644896 da kuma 0044183689.
Ana kuma bin diddigin kuɗin da suka shiga cikin wani akawun na APC da asusu shida da PDP ta buɗe domin tara kuɗin kamfe da na kula da sha’anin jam’iyya.
Kamar yadda doka ta bada dama, EFCC za ta bukaci a aiko mata takardar buɗe akawun ɗin da bayanin kuɗin da suka shiga ko suka fita a cikin shekarar 2021.