Hukumar sojojin Najeriya ta damƙe wani soja kan zargin sana’ar sayarwa ƴan ta’addan makamai da kayan sojoji, mai suna Bala Nura yayin da take bincike kan ɓatan wasu ɗaruruwan Alburusai.

Bayan ya amsa laifinsa, sojan ya faɗi sunayen wasu sojoji da suke aiki tare.
Hukumar ta sanar da kama dakarunta guda uku da ke aikin sayarwa ƴan bindiga makamai a jihar Zamfara.

Wata majiya ta bayyana cewa an kama sojojin ne yayin bincike kan ɓatan wasu Alburusai sama da 400 a sansanin Sojin FOB dake zaune a Shinkafi, jihar Zamfara.

Sojan da aka kama tun farko mai suna, Bala Nura, da ke aiki da barikin FOB, ya amince yana sayarwa ƴan ta’adda makamai har ya yi alkwarin sayar da wasu.
Ya ƙara da bayanin cewa yana sayar da Alburusai 100 masu girman 7.62mm kan kuɗi Naira N100,00. Kuma har sun gama cinikin sayar da wasu guda 1,000 a miliyan ɗaya.
Bayan asirinsa ya tonu, Nura ya bayana sunayen sojoji biyu, Kofur Ehoda Monday, da kuma Kofur, Shehu Mohammed, waɗan da acewarsa suke sana’ar sayar da makaman tare.
Hakan yasa hukumomin soji ƙara matsa kaimi wajen bincike don ƙara zaƙulo duk masu hannu a lamarin idan ba su kenan ba.