JAWABIN KAKAKIN RUNDUNAR ‘YANSANDA NA JIHAR KANO, DSP ANDULLAHI HARUNA GA YAN JARIDA A SHALKWATAR RUNDUNAR DAKE BOMPAI KANO YAU LITININ 11/03/2019.

DANKE MASU KWACEN SAKAMAKON ZABE: A yau Litinin, 11 ga watan Maris shekara ta 2019 da misalin karfe daya na dare rundunar Yansanda ta cafke Kwamishinan kananan Hukumomi na Jihar Kano Murtala Sule Garo da Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa, Lamin Sani a wurin tattara sakamakon zabe na Yankin Karamar Hukumar Nassarawa. Ana zarginsu da kutse cikin cibiyar tattara sakamakon inda suka yi yunkurin lalata takardun sakamakon zaben. Haka kuma jami’anmu sun kubutar da Mai girma mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dr. Nasiru Yusif Gawuna. Tuni an fara kaddamar da binciken wannan abin kaico kuma wannan Runduna na tabbatar wa jama’a cewa duk wanda aka samu da hannu za’a bincike shi da kuma gabatar dashi a gaban kotu.
Muna kira ga jama’a a zauna lafia, Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta (INEC) na kokarin fitar da sakamakon zabubbuka. Kuma mun fahimci yadda wasu magoya bayan jam’iyyu a wannan jiha sun fara bukukuwan murnar cin zabe, ya zama wajibi a jira har sai Hukumar Zabe (INEC) ta kammala tattarawa da bayyana sahihin sakamako. Wannan kira ya zama wajibi don tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da dakile hadura da hargitsi. Duk wanda a ka samu yana tada hankalin jama’a za mu kamashi kuma a gabatar da shi a gaban Sharia.
DSP ABDULLAHI HARUNA,
POLICE PUBLIC RELATIONS OFFICER,
FOR: COMMISSIONER OF POLICE,
KANO STATE.

