Jami’an ƴan sandan babban birnin tarayyar Abuja na ƙoƙarin kwantar da wata tarzoma da ta ɓarke a unguwar Dei-Dei a kasuwar kayan gini a Abuja.

Wani mazauni yankin ya shada wa BBC cewa tarzomar ta samo asali ne bayan da wata babbar mota ta take wata mata da ke kan acaba.
Lamarin da yasa aka ƙone babur ɗin, wanda hakan ya fusata ƴan acaba suka shiga ƙone shaguna da farfasa ababen hawa.

Mazaunin yanki ya bayyana cewa kawo yanzu mutum guda ne aka tabbatar da mutuwarsa sanadiyar rikicin tare da jikkatar wasu da dama.

Rahotanni sun ce rikicin na neman rikiɗewa zuwa na ƙabilanci tsakanin Hausa da ƴan kabilar Igbo.